1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar bakar fata a kasar Tunisiya

Mahmud Yaya Azare M. Ahiwa
April 13, 2023

Dururuwan bakin haure bakar fata, sun yi zanga-zanga a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Tunusiya yayin da ake ci gaba da tsamo bakin haure da suka mutu a Teku.

https://p.dw.com/p/4Q1MM
Zanga-zangar bakar fata a birnin Tunis
Hoto: Hasan Mrad/Zumapress/dpa/IMAGESLIVE /picture alliance

Dururuwan bakin haure bakar fata, sun yi zanga-zanga a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijira da ke Tunisiya, bayan da ya dakatar da shirin sama musu mafaka a kasashen ketare. Sai da 'yan sanda sun yi amfani da barkwanon tsohuwa wajen tarwatsa dandanzon bakin hauren da ke neman a sama musu makoma. Wannan ya faru ne bayan bakin sun yi kokarin kutsawa da karfi cikin ofishin hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Tunis, fadar mulkin kasar ta Tunisiya.

Andu Paatrick, wani dan kasar Ghana da yake da rijistar zama mai neman mafaka, ya ce, abokan zamansa da dama a kasar ta Tunisiya sun shafe shekaru biyu zuwa uku suna neman rijista ba tare da samun nasarar hakan ba, kuma tun bayan jawaban nuna wa bakake kyama da shugaban kasar ta Tuniya ya yi a kwanakin baya, kasar ta zamo wa baki bakaken fata tamkar jahannama.

A farkon watan nan ne na Afrilu dai hukumar ta hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan ba da mafaka a dukkanin ofisoshinta da ke sassan duniya, har sai ta kammala komawa kan sabon tsarin yi wa bakin-hauren rijistar.   

Akwai dai kimanin bakin haure sama da dubu hamsin a kasar Tunisiya, wadanda kuma hukumar kula da kaurar jama'a ta yi musu rijista ba su fi dubu biyar ba.

Bakin haure a halin tsaka mai wuya
Hoto: Jihed Abidellaoui/REUTERS


Kuma kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Tunisiya, Nabeel Ammar ke cewa kasar tasa ba ta gaza ba wajen samawa dubban bakin hauren yanayin da ya dace da su.

"Na yi amamnar cewa, dukkanin hukumomi na iya bakin kokarinsu don ganin wadannan bayin Allah sun samu mafakar da ta dace da rayuwar bil adama. Abin dai da ke faruwa shi ne, jita-jita da ake ta yadawa ce ke razana su, duk da cewa na san ba za a rasa wasu bata-gari da ke kokarin muzguna musu ba. Wannan na iya faruwa a ko ina suke."

Hakan na wakana ne dai a daidai lokacin da ma'aikatan agaji ke ci gaba da tsamo gawarwakin bakin hauren da ke nutsewa a Teku, bakin da ke ci gaba da kokarin shiga kasashen Turai, lamarin da ya kara ta da hankalin Majalisar Dinkin Duniya a ta bakin shugaban hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, IOM, Antonio Vitorino wanda ya siffanta watanni uku na farkon wannan shekara ta 2023, a matsayin lokaci mafi muni ga bakin haure da ke fafutukar tsallaka teku don shiga Turai tun shekarar 2017.