Kungiyar Boko Haram mai alaka da IS a fafutukar kafa daular musulunci, ta tabbatar dauki alhakin kai harin da ya kashe mutane sama da 20 a wasu kauyuka a jihar Diffa na kasar Nijar.
Cikin wani sakon bidiyo da kungiyar ta fitar, an ga wani dan kungiyar sanye da kakin soja rabin fuskarsa a rufe, inda ya yi ikirarin kai harin da harshen hausa tare da barazanar kai wasu hare-hare a yayin bukukuwan kirsimeti.
Tun shekarar 2009 mayakan Boko Haram suka fara barna a Arewa maso gabashin Najeriya, sama da mutane 36,000 sun mutu yayin da kungiyar ke cigaba da barazana a kasashen Nijar da Kamaru da Chadi duk da alkawarin gwamnatoocin na murkushe tasirin kungiyar.