Batutuwa da suka dau hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 16.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Batutuwa da suka dau hankalin jaridun Jamus

Zubar da jini lokacin azumi da gallabar Boko Haram sun dau hankali a jaridun Jamus.

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus akan nahiyar Afirka ta Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. A sharhinta mai taken sannu cikin lokaci za'a magance Boko Haram. Jaridar ta yi tsokaci da wata hira da aka yi da Shugaban Nijar Mahammadou Issofou wanda ya jaddada kudirin hadin gwiwa da kasashen Yamma wajen magance matsalolin tsaro da ta'addanci a kasashen Sahel da suka hada da Chadi da Mali da kuma Libya wadanda ke makwabataka da Nijar.

Jaridar ta ce kalubalen Boko Haram magana ce ta lokaci kamar yadda Muhammadou Issoufou ya nunar bisa la'akari da sakamakon mai kyau da ake samu yanzu haka a yaki da kungiyar.

Hannu daya aka ce baya daukar jinka, akwai bukatar hada karfi da karfe wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda kamar 'yan al'Kai'ida a yankin Maghreb da 'yan Daesh ko IS masu da'awar Jihadi. A cewar Issofou hadin gwiwar kasashe biyar na yankin Sahel karkashin inuwar kungiyar G-5 Sahel da suka hada da Mali da Mauritaniya da Burkina Faso da Chadi da Nijar sun kaddamar da namijin kokari na ganin an yaki ta'addanci da tabbatar da tsaro a fadin yankin.

Jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce a matakin bani gishiri in baka manda, kungiyar Tarayyar Turai za ta taimakawa da kasashen na Sahel da tallafin kudi yayin da su kuma za su tabbatar da tsaron iyakokinsu domin dakile kwararar bakin hauren da kuma yaki da ta'addanci.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung a sharhinta mai taken zubar da jini a cikin watan Azumi. Jaridar ta ce mutane fiye da 20 aka kashe a wani harin kunar bakin wake a Mogadishu da aka dora alhakinsa akan kungiyar al-Shabab. Jaridar ta ce a wannan lokaci na Ramadan 'yan kunar bakin wake su kai hari abin damuwa ne matuka bayan lafawar hare hare a Mogadishu tun daga watan Mayun da ya gabata.

Ta ce duk da kokarin kasashen duniya, na tallafawa kasar samun zaman lafiya, gwamnatin tsakiyar ba ta da karfi sosai yayin da a waje guda kuma yankin ke neman sake fadawa matsalar fari.

Jaridar ta ce ko da yake an zabi sabon shugaban kasa a yanayi mawuyaci tasirin karfin ikonsa bai wuce iya Mogadishu ba. al Shabab har yanzu ta na rike da yankunan karkara ta na kuma kokarin cigaba da kai hare hare babban birnin kasar.

A wani sharhi mai taken hasashen managarcin cigaba a Afirka. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce a wannan shekarar akwai kyakkyawan fata za'a sami cigaba sosai a Afirka fiye da shekarar 2016 da aka sami karayar tattalin arziki.

Bayanin wanda aka fitar a karshen nazarin binciken cigaban tattalin arzikin Afirka da hadin gwiwar Bankin raya kasashen Afirka da kungiyar kawancen tattalin arziki da raya kasashen Turai OECD da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka gudanar da aka gabatar a Berlin ya nuna baki daya tattalin arzikin Afirka zai bunkasa daga 2.2 cikin dari a bara zuwa kashi 3.4 a bana yayin da a shekara mai zuwa ake hasashen tattalin arzikin na iya samun cigaba da kashi 4.3 cikin dari.