Azumi mai dogon zango a Jamus | Zamantakewa | DW | 29.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Azumi mai dogon zango a Jamus

Yanayin azumin watan ramadan a wasu kasashen nahiyar Turai ya sha bambam da na kasashen Afirika. A nan Jamus Musulmi kan yi azumin ne na tsawon sa'oi 19 zuwa 20.

Musulmi na yawaita ibada a yayin azumin Ramadan.

Musulmi na yawaita ibada a yayin azumin Ramadan.

Lokacin azumin watan Ramadan lokaci ne da daukacin Musulmin duniya ke kame bakin su daga ciye-ciye da shaye-shaye da ma saduwa da iyali, daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana har na tsawon wata guda. A nan Jamus Musulmi na yin azumi mai tsahon gaske, sai dai hakan bai hana ma'aikata masu azumin zuwa wuraren aikinsu ba. Shin ko ya ma'aikatan ke hada aikinsu da azumin?

Shagon sayan kayan masarufi na Turkawa da ke Bonn

Shagon sayan kayan masarufi na Turkawa da ke Bonn

Koda yake azumin na da tsahon gaske, ga Malam Iddi Ismaela dan asalin kasar Yuganda mazaunin Jamus ba shi da matsala da zuwa aiki da azumi a bakinsa domin abin da ya saba yi ne akalla sau biyu a mako:

Yanayin da mutane kan dauki azumi

"Azumi ya danganta da yadda mutum ya dauke shi, idan ka dauke shi da wahala to tabbas zai wahalar da kai, amma idan ka dauke shi a matsayin ibada da kuma lafiyarka, to zai zo maka cikin sauki"

Ko yaya kasuwanni ke ci a wannan wata mai alfarma na Ramadan? Ocak Markwani shagon Turkawa ne da ake sayar da kayan abinci kama daga nama da sauran kayan masarufi musamman na bukata yayin azumi. Daya daga cikin ma'aikatan wajen ya yi karin haske:

"Farkon azumi mun sami kasuwa sosai kasancewar mai azumi na son in ya zo buda baki ya ci wannan ya sha wancan, amma yanzu abin ya canza ba kamar farkon azumin ba."

Buda baki a masallatai

Masallacin Almuhajirin da ke cikin birnin Bonn, na daya daga cikin masallatai da mutane ke taruwa domin yin buda baki, shugaban masallacin ya bayana yadda suke gudanar da al'amuran buda bakin.

Buda baki na bai daya yayin azumin Ramadan a Masallatai

Buda baki na bai daya yayin azumin Ramadan a Masallatai

"A wannan watan muna ciyar da masu azumi, cikin masu zuwa akwai dalibai da leborori har ma da 'yan fensho. Wata rana ana cin kaza wata rana kuma shinkafa da naman rago. A Musulunce duk wanda ya ciyar da mai azumi yana da lada daya da mai azumin, don haka mutane da dama na kawo taimako don ciyar da masu azumin."

Za a dai kwashe kimamin shekaru biyar nan gaba azumin watan Ramadan na kamawa a lokacin bazara a kasashen Turai, inda tazarar da ke tsakanin ketowar alfijir da kuma lokacin buda baki ke kai wa tsahon sa'oi 19 zuwa 20.