1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta tura ƙarin sojoji zuwa Somaliya

August 23, 2010

An daɗa yawan dakarun wanzar da zaman lafiya a Somaliya.

https://p.dw.com/p/OuPc
Sojojin AU masu aikin sintiri a Mogadishu.Hoto: AP

Sojojin wanzar da zaman lafiya a ƙarƙashin lemar Ƙungiyar Gamayyar Afirka(AU) sun isa Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato wani jami'in ƙungiyar ta AU da ya tabbatar da isan ɗaruruwan sojojin a Mogadishu yana cewa sojojin sun fito ne daga Uganda. A watan jiya ne dai Uganda ta yi alƙawarin ƙara yawan sojojinta zuwa dubu 2 a Somaliya, bayan harin da ƙungiyar al-Shabaab ta kai Kampala wanda ya kashe mutane 70.Tun a shekara ta 2007 ne dai ƙungiyar al-Shabaab mai alaƙa da ƙungiyar al-Ƙa'ida ke yaƙi da gwamnatin riƙon ƙwaryar Somaliya. A taron shugabannin ƙungiyar AU da aka gudanar a birnin Kampala na Uganda, AU ta sha alwashin ƙara yawan sojojinta´domin tabbatar da tsaro a Somaliya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita Halima Balaraba Abbas