APC: ″Ku binciki yarjejeniyar bogi da Boko Haram″ | Siyasa | DW | 03.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

APC: "Ku binciki yarjejeniyar bogi da Boko Haram"

Jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta bukaci a gudanar da cikakken bincike a kan abin da ta kira yarjejeniyar sulhun da gwamnati ta cimma da jabun 'ya'yan kungiyar Boko Haram

Jamiyyar adawar ta APC a Najeriyar ta bukaci da a gudanar da bincike na musamman a kan wannan batu na shellar tsagaita wuta da gwamnati ta sanar a makonnin baya, domin gane gaskiyar wannan lamari da take wa kalon tamkar yaudara ce ga ‘yan Najeriya.

Daukacin batun dai ya afka cikin yanayi na rudani rashin tabbas da ma harzuka da mafi yawan al'ummar Najeriya suka yi bisa kan dagewar da gwamnati ta yi kan batun, musamman bayan da karara a fili shugaban kungiyar Ahlu Sunnah Li Da'awatti Waljihad, Imam Abubakar Shekau ya ce babu fa wani batu na sulhu da

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar

Manyan jagororin jam'iyyar APC

suka cimawa da kowa. Malam Lawalli Shuaibu shine mataimakin shugaban jamiyyar APC mai kula da yankin arewacin Najeriya.

"Abin da ya sa muka ce a bincika saboda gwamnati da shi mai magana da yawun bakin shugaban kasa da kuma hafsan hafsoshin soja duk mun gansu a telbijin suna bayanin yadda aka kai wannan batu na tsagaita wuta. Muna kokarin bai wa gwamnati shawara a kan wannan matsala amma sun budi baki sun ce mana ‘yan Boko Haram ne, to yaya zamu yi masu saboda haka muna son a bincika".

Martanin gwamnati dangane da zargin 'yan adawa

Na yi kokarin jin ta bakin jami'an gwamnatin Najeriya don jin shin me za su ce da wannan bayani daya fito a kan batun yarjejeniyar da suka dade da cewa lallai suna tattaunawa amma da na tuntubi Mr Mike Omeri shugaban cibiyar samar da bayanai ta aiyyukan ta'adanci ya ce suna taro a kan lamarin kuma za su sanar da matsayinsu a nan gaba. Mallam Kabiru Adamu kwararre ne a fanin tsaro a tarayyar Najeriyar.

"An samu koma baya sosai domin idan da gwamnati za ta fito ta ce haka ne akwai batun sulhu duk da dai akwai wadanda ba za su yarda ba, to yanzu gaskiya sai ta kara himma wurin gamsar da jama'a har jama'a su san akwai wani ci gaba, to ai kaga akwai koma baya. Kuma ai yadda su wakilan gwamnati suka nuna shine cewa ai ‘yan kungiyar sun tsagaita wuta, amma shaidar me ake da shi cewa sun tsagaita wutar? Kar ka manta su ‘yan Jama'atu Sunnah Li Da'awati Wal Jihad sun yi amfani da wannan dama da suka samu har sun kame wuri kamar Mubi".

Abin jira a gani shine mataki na gaba da gwamnatin ke tunanen dauka a yanzu da aiki ya koma danye a kokarin gwama amfani da karfi da kuma hanyar sulhu wajen shawo kan wannan matsala.

Sauti da bidiyo akan labarin