1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Cutar kwalara ta kashe mutane 13 a Maradi

Salissou Boukari MNA
August 11, 2018

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa annobar cutar kwalara da ta barke a cikin jihar Maradi ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 kaman yadda cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ta OCHA a Nijar ta sanar.

https://p.dw.com/p/330Qb
Krankenhaus von Bukavu RD Kongo Cholera  Afrika
Hoto: DW/el Dorado

Wadanda suka kamu da cutar ta kwalara da yawansu ya kai kimanin mutum 50 an same su ne wasu har ma a cikin wasu unguwannin birnin na Maradi, kuma akasarinsu yara ne 'yan daga shekara daya zuwa shekaru 15 da haihuwa a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Mutane uku na farko da suka kamu da cutar ta kwalara an gabatar da su a asibitin N'Yelwa a daran hudu zuwa biyar ga watan Yuli da ya gabata, kuma an fito da su ne daga garin Jibiya na Tarayyar Najeriya mai makwabtaka da jihar ta Maradi. Ya zuwa ranar bakwai ga watan nan na Agusta, an samu kimanin mutane 993 da suka kamu da cutar ta kwalara cikinsu ne aka samu mutun 13 da suka mutu a cewar ma'aikatar ta Majalisar Dinkin Duniya ta OCHA a Jamhuriyar ta Nijar.

Matakin gaggawa da gwamnatin Nijar ta dauka tare da ban hannun hukumar lafiya ta duniya WHO, da UNICEF da kungiyar likitoci ta duniya wato MSF, sun sa an samu takaita yaduwar cutar a cewar ministan kiwon lafiya na kasarNijar Iliassou Mainassara.