Annobar cutar coronavirus a duniya | BATUTUWA | DW | 19.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Iftila'in coronavirus a duniya

Annobar cutar coronavirus a duniya

Kasashen duniya sun kara azama wajen yaki da cutar coronavirus yayin da a waje guda aka sami karuwar mace mace a sakamakon cutar a nahiyar Turai.

A kasashe da dama an sami karuwar mace mace a sakamakon yaduwar cutar coronavirus inda wasu kasashe suka rufe iyakokinsu domin dakile yaduwar cutar.

Kasar Italiya a cewar Firaminista Giuseppe Conte za a tsawaita wa’adin rufe iyakoki da takaita zirga zirgar jama’a.

Mutanen da suka kamu da kwayar cutar sun hauwa mutum 200,000 a fadin duniya baki daya.

A Jamus shugabar gwamnati Angela Merkel ta bayyana halin da aka shiga a kasar a matsayin kalubale mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu

Kasashen Afirka ma ba a bar su a baya ba wajen daukar matakan rufe iyakokinsu.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin