An samu bullar Coronavirus a Saudiyya | Labarai | DW | 02.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu bullar Coronavirus a Saudiyya

Yanzu haka an killace mara lafiyan a asibiti, an kuma fara tantance wadadan mutumin ya yi mu'amala da su domin gudanar da bincike na gaba.

Hukumomin kasar Saudiyya sun tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus, hukumomin kiwon lafiya sun ce mutumin dan salin kasar ne da ya dawo daga kasar Iran. 

Yanzu haka dai akwai mutane 1,700 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya kadai.