An samu Covid-19 a wasu kasashen Afirka | Labarai | DW | 13.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu Covid-19 a wasu kasashen Afirka

A karon farko Ghana da Gabon sun tabbatar da samun mutane da suka kamu da coronavirus, abin da ya kai kasashe 10 ke nan da cutar ke cikinsu a kasashen Afirka bakar fata.

A Ghana hukumomin kasar sun ce wasu 'yan kasar biyu ne suka kamu bayan dawowa daga Norway da kuma Turkiyya.

A Gabon kuwa wani dan kasar da ya ziyarci Faransa ne aka samu da matsalar da a yanzu ta zama annoba gama duniya.

Kasashen Ivory Coast da Najeriya da Senegal da Kamaru da Togo da Afirka ta Kudu, na daga cikin kasashen Afirkar da aka samu wadanda suka kamu.

Haka ma hukumomi a Burkina Faso da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun tabbatar da samun wadanda ke dauke da cutar ta Covid-19.

Afirkar ce dai har yanzu ke da karancin wadanda ke dauke da cutar idan aka kwatanta da yadda take yaduwa a duniya, musamman a yankunan Asiya da kuma Turai.