Masana sun ce yaduwar cutar Coronavirus za ta ragu | Siyasa | DW | 28.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Masana sun ce yaduwar cutar Coronavirus za ta ragu

Masana kwayoyin cututtuka sun yi bayanin cewar cutar Coronavirus za ta yi sauki da zarar an shiga yanayi na zafi, wato ke'nan karfinta na raguwa a yankuna masu zafi.

Fatan da ake yanzu shi ne abubuwa za su kyautatu a lokacin zafi a kasashen Turai. Ita dai sabuwar cutar nan ta Coronavirus tana da kamanceceniya da kwayar cutar virus da ke haddasa matsananciyar mura, wanda haka ke nufin za ta yi sauki a lokacin da zafi ke karuwa kamar yadda murar ke yin sauki da zarar an fita lokacin sanyin hunturu a Turai. Thomas Pietschmann kwararren masanin kwayoyin cututtuka a cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa da ke birnin Hannover na nan Jamus ya ce ko da yake ba za a iya yanke hukunci ba ko cutar za ta yi sauki kamar yadda aka yi fata, amma bincike ya nuna karfinta na raguwa a lokacin zafi. Ya ce: "Zafi mai yawa da yanayi na lema na taka rawa wajen yaduwa da kuma karfin cutar. Ta fi yaduwa cikin yanayi mai sanyi da karancin lema a cikin yanayi." Masanin ya kara da cewa wani kitse da ya kewaye kuma yake kare Coronavirus yana narkewa a cikin yanayi na zafi, shi ya sa da zarar ya narke sai cutar ta rage karfi. 

 Maza sun fi mata kamuwa da cutar Coronavirus saboda karkon garkuwar jiki

Sai dai sabanin kwayar cutar da ke sa mura da za a iya cewa kusan kowa ya taba harbuwa da ita akalla sau daya, amma garkuwar jikin dan Adam ba ta shirya ga wannan sabuwar kwayar cutar ba domin yanzu ne karon farko da dan Adam ya harbu da ita, kamar yadda bayanai daga Chaina suka nunar cewa sau daya ne kwayar cutar ta yadu daga dabba zuwa dan Adam daga nan kuma ta fara yaduwa a cewar masanin. Ko da yake tsanani ko saukin cutar ya dogara ga yawan shekaru da lafiyar jiki wanda ya kamu da ita, amma jinsi na taka rawa a nan inda a dangane da Coronavirus yawan mazan da ta yi ajalinsu ya fi mata, kamar yadda Thomas Pietschmann kwararren masanin kwayoyin cututtuka ya yi bayani. Ya ce: "Kasancewa wasu kwayoyin garkuwar jiki da ke gane jiki ya kamu da cuta na da alaka da kwayoyinn halitta. Kasancewa mata na da kwayoyin halitta na XX maza kuma na XY ko X da Y. Kasancewa cutar na farma X guda daya, to mace za ta saura da X amma namiji ko zai tashi a tutar babu." Masanin  ya kara da cewa kwayoyin halittar haihuwa da mata ke da su na taimakawa wajen kara musu garkuwar jiki daga cutar. 

Sauti da bidiyo akan labarin