An yi garkuwa da wani Bajamushe a Nijar
April 12, 2018Talla
Jami'i da ke aiki da wata kungiya ta agaji an kama shi a kusa da Ayorou a yankin Tillaberi yankin da ke kara fiskantar hare-hare kan jami'an tsaro da sansanoni na 'yan gudun hijira. Kuma jami'in dan asalin Jamus ya gamu da wannan matsala ce lokacin da yake dawowa daga Ayorou kamar yadda Jando Rhichi Algaher ya fada wa kamfanin dillancin labaran AFP ta wayar tarho.
Ma'aikacin dai da abokan aikinsa sun fada wa mahukunta cewa za su yi tafiyar da safiyar ta Laraba acewar direbansu, sai dai lokacin da suke dawowa 'yan bindigar a babura hudu sun tsaresu inda suka yi gaba da jami'in daga Jamus bayan lallasa masu duka suka kuma kona motar.