1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tashi taron ministocin kudi na G20 baram-baram

Binta Aliyu Zurmi
March 1, 2024

An watse taron ministocin kudi na kasashen masu karfin tattalin arziki na G20 ba tare da cimma wata kwakwarar matsaya ba, saboda rarrabuwar kawuna a kan rikicin Hamas da Isra'ila da kuma na kasar Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4d3R3
Brazilien G20 GIpfeltreffen in Rio de Janeiro | Mauro Vieira
Hoto: Mauro Pimentel/AFP/Getty Images

Ministan kudi na kasar Brazil mai masaukin baki, Fernando Haddad ya bayyanawa manema labarai cewar rarrabuwar kawunan da aka samu a tsakanin mambobin na G20 na da nasaba da taron da ministocin harkokin kasashen ketare na G2 da ya gudana a makon jiya, wanda suka tattauna batun rikicin yankunan.

Kungiyar ta G20 ta tafka mahawara a kan yadda za ta kira ci gaba da mamayar Rasha a Ukraine da murya daya. 

A cewar mataimakin ministan kudi na kasar Japan, rikici na da mumunar illa ga tattalin arzikin duniya, wanda yanzu haka halin da ake ciki ya shafi farashin makamashi da na abinci da ma sauransu.

Taron dai ya kammala ne ba tare da cimma wata kwakwarar matsaya ta bai daya ba, wanda kuma hakan ba shi ne karon farko a tarihin kungiyar ba.