Brazil ita ce kasa ta biyar mafi girma a duniya kuma nan aka fi yin harshen Portuguese fiye da kowanne waje a duniya.
Kasar Brazil da ke da arzikin man fetur na daga cikin jerin kasashen da kasar Potugal ta yi wa mulkin mallaka. Yanzu haka ita ce kasar da ta fi kowacce yawan mutane a yankin Latin Amirka. Kwallon kafa na daga cikin irin abubuwan da suka sanya kasar ta shahara.