1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta nuna bukatar shiga kungiyar BRICS

Uwais Abubakar Idris
August 22, 2023

Kasashe da dama ciki har da Najeriya na nuna bukatar shiga kungiyar BRICS ta kasashe masu tasowa ta fuskar tattalin arziki da ke shirin kalubalantar babakeren kasashen yamma

https://p.dw.com/p/4VSfn
Taron kolin shugabannin kungiyar BRICS a Afirka ta kudu
Taron kolin shugabannin kungiyar BRICS a Afirka ta kuduHoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

Kokarin fadada kungiyar ta kasashen BRICS da ya bai wa Najeriyar dama ta bin sauran kasashen da suka nuna sha'awar shiga cikin kungiyar da a yanzu take tashe a tsakanin kasashen duniya musamman masu tasowa, wadanda ke son sauya yadda ake tafiyar da al'amura a duniya. 

Yunkurin nuna sha'awar shiga kungiyar wanda mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ke halartar taron kolin kungiyar a Afirka ta Kudu ya sanya Najeriyar fatar samu shiga jerin kasashen da ke son ganin sauya yadda al'ammura suke wakana.

Najeriyar ta kasance kasar da ke fama da matsaloli da ma kungiyar kasashen Afrika ta yamma ECOWAS da Najeriyar ke jagoranta a yanzu. Farfesa Sdeeq Abba masanin kimiyar siyasar kasa da kasa da ke jami'ar Abuja ya ce lamarin fa da kamar wuya.

Duk da doki da Najeriyar ke yi na shiga kungiyar, wasu masana na ganin cewa akwai wasu manyana kasashe da suka dade suna tasiri a duniya amma basa ciki. Hakan ya sanya suke gani ya kamata Najeriyar ta yi taka tsan-tsan tare da nazarin matakai a sabuwar tafiyar da ake yi. 

Kungiyar kasashen BRICS din da suka haura 40 a yanzu kafin jerin sabbin da suka nuna sha'awa tana son katse zaren manyan kasashen duniya a fanin tattalin arziki, kimiya da fasaha, tsaro da ma ci gaban rayuwa.