SiyasaJamus
Putin ya fasa halartar taron BRICS a Afirka ta Kudu
July 19, 2023Talla
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce yunkurin kama Putin kamar yadda sammacin kotun ICC ta bayar a kan shi, ka iya zama wani mataki na ayyana yaki. Sai dai fadar Kremlin ta nesanta kanta da wadannan kalaman.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne zai wakilci shugaban na Rasha a taron na yini biyu, da zai hadar da kasashen Brazil da Rasha da Indiya da China gami da Afirka ta Kudu.
Kotun ta ICC ka iya kama Mista Putin muddin ya taka kafa a kasar Afirka ta Kudu bisa zargin aikata laifukan yaki a kasar Ukraine.