1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ba ta rabu da rikice-rikice ba

Ubale Musa MAB/SB
June 29, 2023

Wani sabon rahoto bisa batun zaman lafiya a duniya baki daya dai ya ce Najeriya tana zaman kasa ta 21 mafi hatsari a duniya baki daya, ga batun zaman lafiya da kwanciyar ta hankali a shekarar bana.

https://p.dw.com/p/4TFD0
Nigeria, jihar Borno na fama da mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram sun janyo rikice-rikice a NajeriyaHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

 

Rahoton na shekara dai yace tarrayar Najeriyar ta zarta kasashe irin nasu Syria daYemen da Afghanistan da ko dai suka fuskanci yaki gadan gadan, ko kuma ke neman hanyar kauce masa ya zuwa yanzu. Duk da kisan kudi da kara yawa na jami'an tsaron kasar a lokaci na kankane dai har ya zuwa yanzu kasar na kallon sake tashin matsalolin na tsaro walau a yankin arewa maso gabas a inda masu ta'addar ISWAP ke rayuwa irin ta dashi mai rai guda tara, ya zuwa arewa maso yammacin kasar da barayin shanu da mutane ke daukar numfashi.

Karin Bayani: Tashe-tashen hankula suna ta'azzara

Najeriya | 'Yan sanda a Kankara da ke jihar Katsina
'Yan sandan NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Sama da Triliyan 14 ne dai aka kiyasta ita kanta tsohuwa ta gwamnatin kasar d ata shude ta batar a shekaru takwas a laluben zama na lafiya ba tare da kaiwa ya zuwa ga biya na kwalliyar 'yan mulki ba. Kabir Adamu dai na zaan shugaba na kamfanin Beacon Consult dake nazarin batun tsaro a Najeriya ya ce har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabula ba, duk da kashe makuden kudi kuma ya dace sabuwar gwamnatin kasra ta duaki matakin da ya dace da bin shawarrari na masana.

In har kishe kudi da kara jami'ai sun gaza kai wa ya zuwa ga bukata dai, daga duk alamu sabbabin 'yan mulkin cikin kasar na da sauran tafiya kan hanyar iya kai wa ga burge masu zaben da ke zaman jira na shekaru hudu.

Cikin batun rashin tsaron ne dai ita kanta sabuwar gwamnatin Najeriya ta yi dori wajen yakin neman zaben da ya kai ta ga samun damar mulkin kasar. Kuma a tunanin Dr Yahuza Getso da ke sharhi kan batun rashin tsaron, sabuwa ta gwamnatin kasar tana da bukatar tauna tsakuwa ga jagororin tsaron da su kansu jami'an da ke filin daga da nufin aike da sakon neman biyan bukatar da ke zaman mai tasiri ga makoma ta kasar.