An nada mace ta farko ministar harkokin gida ta Burtaniya | Labarai | DW | 28.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada mace ta farko ministar harkokin gida ta Burtaniya

Sabon firaministan Burtaniya Gordon Brown ya nada mace ta farko a matsayin sakatariyar harkokin cikin gida na kasar.

Wanda aka nadan kuwa itace Jacqui Smith yar shekaru 44 da haihuwa daya daga cikin mata yan majalisa su 101 da aka nada lokacinda Blair ya zama firaminista a 1997.

Hakazalika Gordon Brown ya nada wani tsohon mai baiwa Blair shawara a matsayin sakataren harkokin wajen kasar inda ya maye gurbin Magrett Beckett.

Ana sa ran kuma Jack Straw wanda shine kanfe manaja na Brown zai samu matsayin ministan sharia kuma mataimakin firaminista.