An kone motocin ′yan sanda a birnin Yamai | Labarai | DW | 17.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kone motocin 'yan sanda a birnin Yamai

Jami'an tsaro na 'yan sanda a babban birnin na Nijar sun yi amfani da borkonon tsofuwa a wannan Asabar wajan tarwatsa masu zanga-zangar nuna adawa da mujallar Charlie Hebdo.

Hana wannan jerin gwano ya haddasa tashin hankali mai yawan gaske a birnin na Yamai, inda aka kone motocin 'yan sanda guda biyu, tare da kone Coci-Coci akalla guda uku. Sannan daga bisani masu zanga-zangar sun watsu cikin unguwanni suna kona tayoyi da furta kalammai na kyama ga kasar Faransa da kuma mujallar Charlie Hebdo. Tuni dai Jakadan Faransa a Nijar ya yi kira ga 'yan asalin kasar ta Faransa da ke wannan kasa da su yi takatsantsan.

A birnin Maradi ma dai a safiyar wannan Asabar wasu matasa sun kona tayoyi a wasu unguwanni, sai dai jami'an tsaro da ke sintiri cikin birnin sun tarwatsa su. A ranar Jumma'a dai a birnin Damagaram aka gudanar da zanga-zanga mai muni kan wannan batu na nuna adawa da mujallar ta Charlie Hebdo, inda kawo yanzu dai adadin wadanda suka rasu a birnin na Damagaram ya kai na mutum biyar, yayin da wasu kusan 50 suka jikkata.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal