An kama Jamusawa ′yan IS a birnin Mosul na Iraki | Labarai | DW | 18.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama Jamusawa 'yan IS a birnin Mosul na Iraki

A kasar Iraki, sojojin rindunar yaki da ta'addanci a birnin Mosul sun sanar da kame wasu mayakan 'yan jihadi mambobin kungiyar IS guda 20 da suka hada da 'yan asalin kasar Jamus da wasu kasashen Turai. 

A kasar Iraki,sojojin rindunar yaki da ayyukan ta'addanci a birnin Mosul sun sanar da kame wasu mayakan 'yan jihadi mambobin Kungiyar IS guda 20 da suka hada da 'yan asalin kasar Jamus da wasu kasashen Turai. 

Daga cikin wadannan mayaka na Kungiyar IS da aka kama, biyar 'yan asalin kasar Jamus ne. Sauransu kuma 'yan asalin kasashen Kanada da Tchetcheniya da Turkiyya da kuma musamman wasu mata 'yan asalin kasar Rasha. 

Yanzu haka kuma jami'an bincike na neman tantance gaskiyar asalin wata yarinya 'yar shekaru 16 da aka kama daga cikin wadannan mayaka, da kuma ake kyautata zaton 'yar asalin garin Pulsnitz na jihar Saxonny ta kasar Jamus ce wacce ta bace a shekara ta 2016 jim kadan bayan ta karbi addinin Muslunci.