An fara sasanta rikicin Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 26.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara sasanta rikicin Sudan ta Kudu

Shugaban Kenya da Firaministan Habasha suna birnin Juba a wani kokarin yin sulhu tsakanin masu rikici a wannan jaririyar kasa.

Shugaban Sudan ta Kudu Salava Kiir ya fara wata tattaunawa da shugabannin kasashen Kenya da Habasha da nufin kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa a kasarsa. Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn suna Juba babban birnin Sudan ta Kudu a kokarin sasantawa don cimma wani kudurin zaman lafiya. Duk da kiraye-kirayen da kungiyar tarayyar Afirka AU, ta yi na a tsagaita wuta a lokacin bukukuwan Kirsmetti, a ranar Laraba dakarun 'yan tawaye da na gwamnati sun yi arangama a birnin Malakal, babban birnin jihar Upper Nile mai arzikin man fetir. Kasashen yamma da na gabacin Afirka da ke kokarin hana yaduwar rikicin a wannan yanki mai fama da matsalolin tsaro, sun yi ta kokarin yin sulhu tsakanin shugaba Salva Kiir dan kabilar Dinka da jagoran 'yan tawaye Riek Machar dan kabilar Nuer, wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa har zuwa koransa a cikin watan Yuli.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu