An bukaci dakile kwararar ′yan gudun hijira a Turai. | Labarai | DW | 24.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bukaci dakile kwararar 'yan gudun hijira a Turai.

Firaministan kasar Netherland Mark Rutte ya bukaci kasashen gabashin Turai da ke cikin kungiyar EU da su tashi tsaye don dakile kwararowar baki zuwa nahiyar

Mark Rutte Niederlande Premierminister

Mark Rutte

Kalaman na Mark Rutte dai na zuwa ne a dai-dai kammala wata ganawa da ya yi da shugaban kungiyar Donald Tusk, kan yin la'akari da man'yan kasashen da ke cikin kungiyar masu karfin arziki musamman kasar Jamus.

Firimiyan na Netherland, yace kasashen gabashin Turai ba su tabuka wani abin azo agani ba, kan dakile tudadowar 'yan gudun hijira ba, a yayin da a bangarensu, sune ke kashe makudan kudade to amma su basa tabuka komai.

Kasashen Jamus da Suwidin da Netherland, sune daga cikin kungiyar EU ke taka muhimmiyar rawa wajen kula da jin dadin 'yan gudun hijirar, dake kwarara a nahiyar duk kuwa da jan kafar da wasu daga cikin su suke wajen dakile kwararar su.