1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da gurfanad da Mista Taylor a kotun duniya da ke Hague

June 16, 2006
https://p.dw.com/p/Butk

Kwamitin sulhu na MDD ya amince da a gurfanad da tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a gaban kotun ta musamman ta MDD dake birnin The Hague na kasar NL. Yanzu haka dai wata kotun MDD a Saliyo ke yiwa Taylor shari´a bisa zargin aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin dan adam. An dauki wannan mataki ne na canza wurin da ake yiwa Taylor din shari´a saboda dalilai na tsaro. Idan aka same shi da laifi to za´a tura shi a wani kurkuku a Birtaniya. Ana kuma tuhumar tsohon shugaban na Liberia da rura wutar yakin basasan Saliyo.