Amurka ta ce ba za ta amince da shirin nukiliyar Iran ba | Labarai | DW | 15.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka ta ce ba za ta amince da shirin nukiliyar Iran ba

Shugaban Amurka Barack Obama ya sake jaddada kudurin Amurka na kin amincewa Iran ta mallaki makamin nukilya duba da irin hadarin da hakan ke da shi ga duniya baki daya.

Obama ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin inda ya ce Amurka ba ta niyar daukar matakin sojin kan kasar ta Iran dangane da shirin na ta na nukilya domin kuwa matakai na diflomasiyyar da ake amfani da su a hain yanzu dangane da wannan batun ba su da aibu.

To yayin da Obama ke wadannan kalamai, a hannu guda, firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce alamu na nuna cewar Iran za ta iya mallakar makaman nukiliya cikin 'yan watanni masu zuwa sabanin tunin tunanin da Amurka ke da shi na cewar zai iya kaiwa nan da shekara guda kafin Iran din ta iya mallakar makamin, a saboda haka ne ma ya ce Isra'ila za ta iya afkawa Iran din domin hana ta mallakar makamin.

Wannan dai na zuwa ne mako guda kafin wata ziyar da shugaba Obama zai kai kasar ta Bani Yahudu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman