Amirka zata bawa dubban ´yan gudun hijirar Burundi mafaka ta dindindin | Labarai | DW | 18.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka zata bawa dubban ´yan gudun hijirar Burundi mafaka ta dindindin

Amirka ta ce a cikin shekaru biyu masu zuwa zata dauki ´yan gudun hijirar kasar Burundi su kimanin dubu 10, wadanda daukacin su suka tsere daga kasar dake tsakiyar Afirka tun a shekarar 1972 zuwa Tanzania. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen Amirka Tom Casey ya fadawa manema labarai cewa Washington na shirin ba da cikakkun takardun izinin zama cikin Amirka na dindindin ga dubban ´yan gudun hijirar Burundi wadanda ke zaune a sansanoni dake yammacin Tanzania. Mista Casey ya ce sun dauki wannan mataki ne don amsa kiran hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD. Ya ce bayan sun shiga kasar, daga baya ´yan Burundi ka iya neman takardun fasfunan Amirka. Burundi dai ta yi ta fama da yake yaken basasa tun bayan samun ´yancinta daga Belgium a shekara ta 1962.