Burundi kasa ce wadda Beljiyam ta yi wa mulkin mallaka kafin samun 'yanci a shekarar 1962, kuma Bujumbura ke zama babban birnin kasar.
Kasar ta kan fuskanci rikici tsakanin manyan kabilu biyu na Hutu da Tutsi, duk da yake sau da yawa akwai kwarya-kwaryar zaman lafiya. Kasashen Afirka sun sha yunkurin tabbatar da zaman lafiya a kasar.