Amirka ta nuna shirin zama kan teburin shawarwari da Iran | Labarai | DW | 31.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta nuna shirin zama kan teburin shawarwari da Iran

A takaddamar da ake yi dangane da shirin nukiliyar Iran, Amirka ta koma ga goyon bayan bin hanyoyin diplomasiya don warware wannan kiki-kaka da ake fuskanta. A halin yanzu Amirka ta yi tayin yin tattaunawa kai tsaye da kasar ta Iran mai bin tsarin shari´ar musulunci. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condolezza Rice ta fada yau a birnin Washington cewar a shirye gwamnati ta ta ke yi wannan tattaunawa, amma bisa sharadin cewar Iran ta dakatar da dukkan aikace aikacen bunkasa sinadarin uranium da ake kai ruwa rana kai.

“A shirye Amirka ta ke ta kara matsa kaimi don ganin an samu nasarar warware wannan takaddama ta hanyoyin diplomasiya. Ina tabbatar da cewa Amirka ta kuduri aniyar zama kan teburi guda da kawayenta na kungiyar EU don ganawa da wakilan Iran, da zarar wannan kasa ta daina dukkan shirye-shiryen ta na inganta sinadarin uranium.”

Shi kuma a lokacin da yake tofa akbarkacin bakinsa dangane da wannan batu shugaba GWB cewa yayi Amirka zata taka rawar jagora wajen neman hanyoyin diplosamiyar warware wannan rikici na shirin nukiliyar Iran. To amma shugaban ya ce dole ne Iran ta ba da kwakkwarar shaidar cewa ta yi watsi da shirin inganta uranium.