1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ADC: Sabuwar alkiblar adawa a Najeriya

July 2, 2025

Daruruwan 'ya'yan jam’iyyun adawar Najeriya sun kaddamar da sabbabin shugabannin jam’iyyar ADC don kalubalantar APC mai mulki a shekarar 2027.

https://p.dw.com/p/4wpko
Nigeria vor Präsidentschaftswahl Yola | Kandidat Atiku Abubakar
Hoto: Radeno Haniel/AP/picture alliance

ADC dai ce ke zaman sabon fata na adawar na tunkarar APC yar mulki dake dada nuna alamun mai d akasar zuwa jam'iyya daya tilo

Daruruwa na yaya na adawa ke nan a lokaci na kaddamar da sababbi na shugabancin jam'iyyar ADC a Abuja. Kuma kama daga Atiku ya zuwa Peter Obi, ko bayan Nasiru El Rufai da Rotimi Ameachi da ma Abubakar na Malami, fitattu na adawar tarayyar Najeriyar daga jam'iyyu daban daban dai sun hadu a wajen tunanin kare mulkin APC mai mulki cikin kasar.

Kombobild | Hauptkandidaten für die nigerianische Präsidentschaftswahlen Bola Tinubu und Atiku Abubakar

Taron da ke zaman irinsa na farko a cikin bainar jama'a dai, ya zamo dama a bangaren masu hadakar na ayyan sabbabin shugabannin jam'iyyar. Senata David Mark da ke zaman tsohon shugaban majalisar dattawa ta kasar kuma dan jam‘iyyar PDP ne dai zai ja ragamar sabuwar jam'iyyar, a yayin kuma da Rauf Aregbesola da ke zaman tsohon minista a gwamnatin Buhari, kuma dan APC zai zamo sakataren riko cikin harkokin ADC.

'Yan ADC dai na taron na Abuja ne a cikin yanayi da ya tilasta musu sauyin zauren taron a wani abun da ke nuna alamun kokarin murde wuya a bangaren masu mulki na kasar. To sai dai kuma babu gudu babu jada baya cikin burin nasu a fadar Abubakar Malami da ke zaman tsohon minista a gwamnatin kasar

Nigeria | PDP Präsidentschaftswahl
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Koma ta ina 'yan ADC ke shirin su fara dai babban kalubale da ke a gabansu dai na zaman hadiye maita wajen babban burin kare ikon APC na shekaru dai dai har 12. Kuma kama daga shi kansa Atiku Abubakar ya zuwa ga Rotimi Amaechi da ma Peter Obi da El Rufa'I dai kowa baya boye neman shugabancin kasar a karkashi na sabon tsarin.

Duk da tsallen murna da haihuwar ADC daga dukkan alamu da akwai tafiyar hawainiya cikin tunanin a hadin. Sanata Datti Baba Ahmed dai na zaman jigon jam'iyyar Labour, wanda kuma ya ce kallo ne ya kai shi zuwa zauren taron. An kuma kai ga digon danbar ADC cikin wani sabon rikici a tsakanin tsofaffin 'ya'yan jam'iyyar. An dai ruwaito wasu a cikin jiga jigan ADC suna fadin basu shirin cinikin jam'iyyar. Abun jira a gani dai na zaman iya kaiwa ga hadiye maitar wajen tunakarar APC da ke kara nuna alamun dinkewa wuri guda a bayan Tinubu.