Najeriya: Me ya sa kalaman Tinubu suka harzuka 'yan adawa?
June 13, 2025
Manyan jam'iyun adawa na Najeriya sun nuna bacin ransu a kan kalaman da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar bikin dimukradiyya inda ya bayyana murnarsa a kan matsalolin na rashin jituwar da jam'iyun adawar Najeriyar ke ciki, shugaban ya kaiga tsokanarsu a jawabin nasa. Mecece illar rashin samun adawa mai karfi ga dimukurdiyyar Najeriyar?
Manyan jam'iyun adawar dai sun kaiga harzuka da kalaman na shugabaBola Ahmed Tinubu da ya yi a yanayi na barkwanci da ya koma tamkar shagube bisa ga halin da jam'iyun adawar kasar suka samu kansu a ciki. Wasnnan ya baiwa shugaban Najeriyar damar bayyana cewa yana murna da rikicin da suke fuskanta, kuma ba zai taimaka masu su kintsa gidansu ba.
Tuni masharhanta ke maida martani a kan wannan al'mari ganin shugaban Najeriyar ya kaiga fitowa fili ya bayyana matsayinsa a kan wannan batu bayan nisanta kansa da zargin mayara da Najeriyar kasa mai jamiyya daya tilo.
To sai dai ga jam'iyar APC mai mulki na ganin wannan batu ne na jam'iyun adawar su san mafita, domin dabara ce ta rage ga mai shiga rijiya, domin a yanayi na siyasa ko wane bangare na kokarin ganin yadda zai samu nasara ne musamman a dai dai lokacin da ake tunkarar zaben 2027.
Kama daga babbar jam'iyar adawa ta PDP ya zuwa Labour da ma sauran kananan jam'iyu duka kanwar ja ce ta rikici takaddama darashin jituwa a tsakanin 'ya'yan jam'iyar. A wasu jam'iyun an kai ga samun bangarori a wasu jam'iyun adawar. Mecece illar rashin samun adawa mai karfi ga dimukradiyyar Najeriyar, sanin cewa adawa ita ce gishikin tafarkin mulkin farar hula?
Kwararru na bayyana wannan batun a matsayi kalubale ga jam'iyun adawar Najeriyar muddin suna son yin tasiri a fagen siyasar kasar da a baya suka kasance masu jan hankalin al'umma har da samun nasara a kan gwamnati da ke kan mulki inda kafin kuri'a ya danne na mulki.