Ƙura ta lafa a ƙasar Guinee | Labarai | DW | 26.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙura ta lafa a ƙasar Guinee

A yayin da al´ummar ƙasar Senegal ke cikin jiran sakamakon zaben shugaban ƙasa, su kuwa mutanen Guinee na jiran shugaban ƙasa Lansana Conte, ya naɗa saban Praminista.

Idan dai ba a manta ba,ranar jiya a ka cimma yarjejeniya tsakanin fadar mulkin Conakry da ƙungiyoyin ƙwadago, da jam´iyun adawa, wadda a sakamakon ta, Lansana ya soke sunan Eugen Camara, praminsitan da ya naɗa, wanda kuma bai samu goyan baya ba, daga ƙungiyoyin fara hulla.

Sannan, ya alkawarta naɗa saban paraminista, daga jerin sunayen mutane 5, da yan adawa da kuma ƙungiyoyin fara hulla, za su gabatar masa.

A sakamkon wannan yarjejeniya, ƙasar ta fara komawa hayyacin ta, bayan rigingimun fiye da wata guda, wanda kuma su ka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Ƙungiyoyin ƙwadago, sun ɗage yajin aikin da su ka shirya, na sai illa ma sha Allahu.

Saidai a cewar magudunyan adawa, Mamadou Ba, har yanzu ba a rabu da bukar ba, domin a cewar sa, shugaba Lansana Conte, mazari ne, wanda ba a san gaban sa ba, a saboda haka, a ko wane lokaci, ya na iya saɓa alkawarin da ya ɗauka.