ƙura rikici ta lafa a kasar Congo | Labarai | DW | 23.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ƙura rikici ta lafa a kasar Congo

Hankula sun fara kwanciya a Jamhuriyar dimokraɗiyar Congo bayan da bangarori biyu na magoya bayan shugaban ƙasar Joseph Kabila dana mataimakin sa Jean Pierre Bemba suka sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta janye yan bangar su daga tsakiyar birnin Kinshasa. Dakarun kiyaye zaman lafiya na gamaiyar ƙasa da ƙasa sun shiga birnin domin tabbatar da doka da oda bayan. Majalisar ɗinkin duniya ta yi kira ga magoya bayan yan takarar biyu wadanda ke neman kujerar shugabancin ƙasar Congo su kaucewa dukkan wata fitina da zata tada hankalin jamaá. Ɗauki ba Daɗi tsakanin ɓangarorin biyu tun bayan da aka sanar da sakamakon zabe a ƙasar a ranar Lahadin data gabata ya hallaka a kalla mutane 14 a birnin Kinshasa yayin da wasu mutanen da dama suka sami raunuka.