Ƙungiyar Hizbulahi ta sake harba rokoki zuwa garin Haifa a arewacin Isra’ila. | Labarai | DW | 23.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar Hizbulahi ta sake harba rokoki zuwa garin Haifa a arewacin Isra’ila.

Ƙungiyar Hizbullahi, wadda Isra’ilan ke yaƙa a ƙasar Lebanon, ita ma ta ci gaba da harba rokokinta zuwa ƙasar Bani Yahudun. Rahotannin baya-bayan nan da muka samu sun ce, mayaƙan ƙungiyar sun harba rokokin nan ƙirar Katusha da dama yau, zuwa birnin Haifa, mai tsahar jirgin ruwa, inda a ƙalla mutane biyu suka rasa rayukansu, sa’annan wasu biyar kuma suka ji munanan raunuka. Rahotannin sun ƙara da cewa rokokin sun faɗo a yankuna daban-daban na birnin. Kawo yanzu dai Hizbullahin ta harba rokoki kusan dubu zuwa arewacin Isra’ilan tun da aka fara wannan rikicin, kwanaki 12 da suka wuce.

A ɓangaren Isra’ilan, yawan fararen hular da suka rasa rayukansu sakamakon harba rokokin da Hizbullahin ke yi mata, ya kai 17. Sa’annan kuma, sojojinta 20 ne ’yan Hizbullahin suka kashe, a ɗauki ba daɗin da suke yi a kan iyakar Lebanon.