Ƙasar Siriya ta zargi Amirka da ɗaure wa Isra’ila gindi wajen halaka ’yan ƙasar Lebanon. | Labarai | DW | 23.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasar Siriya ta zargi Amirka da ɗaure wa Isra’ila gindi wajen halaka ’yan ƙasar Lebanon.

Ƙasar Siriya ta ce ɗanyen aikin da Isra’ila ke gudanarwa a ƙasar Lebanon zai ƙara tsananta sakamakon ziyarar da sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice za ta kai a yankin Gabas Ta Tsakiya. Jaridar nan Tishrin mai kusanta da mahukuntan Siriyan, ta buga wani rahoto yau, inda ta ce babu shakka danyen aikin Isra’ila a Lebanon zai ƙara haɓaka bayan ziyarar Rice, saboda ziyarar dai, wato wata sanarwa ce da Amirka ke yi ta nuna cewa yaƙin Lebanon ɗin, nata ne amma wanda Isra’ila ke yi mata.

A cikin wata fira da ya yi da jaridar ABC ta ƙasar Spain, ministan yaɗa labarai na ƙasar Siriyan, Moshen Bilal, ya yi gargaɗin cewa, kutsawar Isra’ila cikin Lebanon za ta iya janyo ƙasarsa cikin rikicin.