Ziyarar shugaban kasar Kenya a Jamus | Siyasa | DW | 29.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar shugaban kasar Kenya a Jamus

Shugaba William Ruto ya yi kira ga gwamnatin Chaina da ta yi amfani da dangartakarta da Rasha a shawarta Putin kan ya dakatar da mamayar Ukraine.

Shugaba William Ruto na Kenya

Shugaba William Ruto na Kenya

Shugaba William Ruto na kasar Kenya yana wata ziyara a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, ziyarar na zuwa a daidai lokacin da ake samun zanga-zangar tsadar rayuwa a kasar Kenya. Shi dai Shugaba Ruto mai shekaru 56 da haihuwa wanda ya dauki madafun ikon kasar ta Kenya a shekarar da ta gabata, ya yi wata fira da DW in da ya yi bayanai kan kan mahimamcin wannan ziyara a birnin Berlin na Jamus.

Shugaban kasar ta Kenya ya nemi ganin sasantawa game da rikicin Ukraine sakamakon kutsen Rasha, abin da zai kawo karshen yuwuwar wani munmunan yaki tsakanin kasashe duniya, inda ya nuna fata kan Chaina za ta taka rawa wajen warware rikicin. Lamarin da ya shafi tsadar rayuwa musamman a kasashe masu tasowa.

Shugaban kasar Jamus Walter Steinmeier da takwaransa William Ruto na Kenya

Shugaban kasar Jamus Walter Steinmeier da takwaransa William Ruto na Kenya

Kan halin da kasarsa ke ciki na zanga-zanga kan matsalar tsadar rayuwa kuwa, Shugaba Ruto ya yi fatalin da batun yana mai cewa, wannan zanga-zangar siyasa kan lashe zaben shugaban kasa da ya yi na shekarar da ta gabata ne, kuma akwai 'yan adawa da ke ci gaba da yi masa irin wannan yankan bayan.

Lokacin zaben na Kenya an yi fafatawa mai zafi tsakanin jagoran 'yan adawa Raila Odinga da kuma William Ruto wanda ya yi nasara. Odinga ya zargi mataimakin shugaban kasar ta Kenya na yanzu Rigathi Gachagua da amfani da jami'an tsaro domin tozarta magoya bayan 'yan adawa, wadanda suka yi zanga-zanga kan nuna takaici da tsadar rayuwa da ake fuskanta.

Sauti da bidiyo akan labarin