Kenya kasa ce da ke yankin gabashin Afirka kuma bisa ga kididdigar da hukumomi suka yi, kasar na da yawan mutanen da suka kai miliyan 45.
Kasar ta samu 'yanci kanta daga hannun Turawan mulkin mallaka na Burtaniya a shekarar 1963. Yanzu haka dai Nairobi shi ne babban birninta. Tattalin arzikin Kenya shi ne mafi karfi a gabashi da tsakiyar Afirka. Kasar ta yi iyaka da Sudan ta Kudu da Tanzaniya da Habasha da Yuganda da kuma Somaliya.