1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar manyan shugabanin Turai biyu a Libiya

September 15, 2011

Frime Ministan Burtaniya David Cameron da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy wadanda suka kasance kan gaba wajen daukan matakin soji a kan Libiya na ziyarar wucin gadi a kasar

https://p.dw.com/p/12ZR0
David Cameron da Nicolas SarkozyHoto: AP

Frime Ministan Burtaniya David Cameron da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy sun kama hanyar zuwa Libiya a wannan alhamis, a cewar jami'ai a  gwamnatin wucin gadin kasar, wato NTC. Shugabanin Turan biyu ne suka jagoranci kirar da aka yi wa kaungiyar kawance ta NATO ta kai hari a Libiya, matakin da ya taimakawa dakarun 'yan tawayen kasar wajen hambarar da Kanar Gaddafi a watan da ya gabata. To sai dai rashin kama Gaddafin da fadace-fadacen da ake yi a yankunan da ke kewaye da garuruwan da har yanzu ke da magoya bayan tsohon shugaban na cigaba da zama kalubale. A halin da ake ciki kuma Shugabanin gwamnatin wucin gadin Libiya na zargin alummar kasa da kasa da yin jinkiri wajen cire hannu akan kaddarorin kasar. A ranar laraba Burtaniya ta fitar da wani daftarin kudurin doka inda ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta sassauta takunkumin da ta sanya wa hukumar man fetur da kuma babban bankin Libiyan.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Umaru Aliyu