1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan zuba jari

Lateefa Mustapha Ja'afar SB/AH
February 19, 2024

A Najeriya ana cin-hanci bayan kammala gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka AFCON duk da cewa ana tsallen murna kungiyar Super Eagles ta samu matsayi na uku a nahiyar Afirka bayan tsawon lokaci.

https://p.dw.com/p/4cZmu
Katar Doha | Schwimmweltmeisterschaften 2024
Hoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

 

Hukumar Kula da Wasannin Linkaya ta Duniya wato World Aquatics, na ci gaba da tsayawa kan bakanta na dakatar da haramcin da ta yi wa 'yan wasan Rasha da makwabciyarta kana babbar aminiyarta Belarus shiga domin a fafata da su a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya wato Olympics. Hukumar ta World Aquatics ta jaddada matsayar tata ne, duk kuwa da cewa akwai yiwuwar wasu shararrun 'yan wasan da suka yi fice a duniya daga kasashen biyu su kauracewa wasannin na Olympics da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa. A watan Satumbar bara ne dai Hukumar Kula da wasannin Linkayar ta World Aquatics ta amince da dage takunkumin da ta kakabawa kasashen biyu, biyo bayan mamayar da Rasha ta yi wa makwabciyarta Ukraine a watan Fabarairun 2022.

Karin Bayani:AFCON: Côte d'Ivoire ta ciri Tuta

Jannik Sinner
Jannik SinnerHoto: Asanka Brendon Ratnayake/AP/picture alliance

Zakaran gasar kwallon tennis ta Australian Open Jannik Sinner ya samu nasarar lashe kyautarsa ta farko ta gasar Rotterdam Open, wanda hakan ya karya lagon kokarin kare kambunsa da shahararren dan wasan kwallon Tennis na Australiya Alex De Minaur ke yi da ci bakwai da biyar da kuma shida da hudu. Wannan nasarar ta kara kaimin dan kasar Italiyan Sinner wanda ya buga wasannin 15 ba tare da an yi nasara a kansa ba, abin da ya daga darajarsa zuwa matsayi na uku a jadawalin shahararrun 'yan wasan tennis din a duniya.

Ita kuwa fitacciyar 'yar wasan tennis ta duniya Iga Swiatek ta sake samun nasarar lashe kofin Qatar Open ne a karo na uku a jere. Swiatek ta samu wannan nasarar bayan da ta lallasa takwarrarta Elena Rybakina da ke a mastayi na hudu a jadawalin 'yan wasan tennis mata na duniya da ci bakwai da shida da kuma shida da biyu a wasan karshe. Mai shekaru 22 a duniya, 'yar kasar Poland din ta kasance 'yar wasa ta farko ta da samu nasarar lashe gasa guda karo uku a jere tun bayan Serena Williams da itama ta lashe gasar Miami daga shekara ta 2013 zuwa 15.

Matakin saka hannun jari a Bundesliga ya haifar da martani
Matakin saka hannun jari a Bundesliga ya haifar da martaniHoto: Moritz Müller/IMAGO

Magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar Jamus, na ci gaba da kawo tsaiko a filayen wasanni sakamakon nuna adawarsu dangane da batun sayar da hannun jarin kungiyoyin Bundesliga da suke yi. Tun bayan da Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafar na Lig-Lig ta Jamus DFL ta cimma yarjejeniya ta biliyoyin daloli da wani dan kasuwa da ke shirin zuba hannun jarinsa a harkar wasannin lig-lig din din wato Bundesliga ne dai, magoya bayan kungiyoyin ke gudanar da zanga-zanga da bore ta hanyar jefa wasu abubuwa da suka hadar da kwallon da ake buga wasan kwallon tennin da shi a filayen wasanni. Shugaban hukumar ta DFL dai, na fatan cewa lamarin ba zai kazanta ba duk da yadda magoya bayan ke ci gaba da nuna adawarsu.

A hannu guda kuma Bayer Leverkusen ta ci gaba da kare matsayinta na farko a kakar wasannin Bundesliga ta bana, bayan da ta lallasa Heidenheim da ci biyu da daya a karshen mako. Wannan nasara dai ta sanya tazarar maki takwas tsakaninta da Bayern Munich da ke a matsayi na biyu da ta kwashi kashinta a hannun Bochum da ci uku da biyu a wasan na mako 22. Bremen ta bi Cologne har gida ta lallasata da ci daya mai ban hashi kamar yadda Hoffenheim ma ta kwashi kashinta a hannu a gida da ci daya mai ban hashi a fafatawarsu da Union Berlin. A karawa tsakanin Wolfsburg da Borussia Dortmund kuwa, an tashi kunne doki ne daya da daya.

'Yan wasan Najeriya
'Yan wasan NajeriyaHoto: Franck Fife/AFP/Getty Images

Duk da cewar martabar Nigeria a matakin kwallon kafa a duniya da nahiyar Afrika ta daga daga inda take a shekarun baya saboda kokarin da kasar ta yi a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka kamala a kasar Cote d'Ivoire, masana da masu fashin baki na ci gaba da sukar yadda harkokin kwallon kafa ke tafiya a kasar. Da yawan ma'abota kwallon kafa na zargin badakalar cin-hanci da rashawa, wacce suke ganin ita ce ta dabaibaye kungiyar ta Super Eagles tare da hana ta katabus wajen samun nasara kamar yadda kungiyar ta yi a shekarun baya.