Zaman lafiyar Gabas Ta Tsakiya | Labarai | DW | 01.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman lafiyar Gabas Ta Tsakiya

Obama na ƙara matsawa Falasɗinawa lamba da su shiga tattaunawa kai tsaye da Isra'ila

default

Shugaban Amirka Barack Obama da shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas, a ganawarsu a birnin Washington

Shugaban Amirka Barack Obama na ƙara matsa lamba kan shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas da ya koma tattauna batun samar da zaman lafiya da Isra'ila. Kafofin yaɗa labarun Larabawa da jami'an Falasɗinawa sun ce, a cikin wata wasiƙa da ya aikewa shugaban na Falasɗinawa, Obama ya faɗawa Abbas cewa ƙin komawa kan teburin shawarwarin ka iya yin mummunan tasiri a hulɗa tsakanin Amirka da Falasɗinu. Tun a ƙarshen shekara ta 2008 shawarwarin samar da zaman lafiyar suka cije. Gwamnatin Falasɗinu na son ta ga wani ci-gaba daga ɓangaren Isra'ila wato kamar daina gina matsugunan Yahudawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kafin ta shiga tattaunawa kai tsaye da ƙasar ta Yahudun Isra'ila.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umar Aliyu