Zaben Najeriya: An kafa dokar hana fita a Bauchi | Siyasa | DW | 29.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben Najeriya: An kafa dokar hana fita a Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 biyo bayan hari da wasu 'yan bidiga suka kai.

Gwamnatin ta Bauchi ta ce ta dau wannan matakin ne don ganin an maido da doka da oda a jihar kuma dokar hana fitar ta shafi kananan hukumomin Bauchi da Kirfi da Alkaleri. Wakilinmu da ke Bauchi din Ado Abdullahi Hazzad ya ce ana zaman dar-dar a sassan da wannan lamari ya shafa.

'Yan bindigar da suka kai hari Bauchi din dai sun yi dauki-ba-dadi da jami'an tsaro a kauyen Dungulbe da sanyi safiyar yau Lahadi. Shaidu sun ce 'yan bindigar sun shiga kauyen ne da misalin karfe goma na safiya, cikin motocin a-kori-kura 20 dauke da muggan makamai.

Wani jami'in soji da ya zanta da kamfanin labaran Faransa AFP ya yi ikirarin cewa sojin sun nakasa maharan wanda ake zaton 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram.