Cika shekaru 30 da MDD ta yi ikirarin 'yancin yara
November 21, 2019Talla
Shekaru 30 bayan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya game da Hakkin yara, kasashe takwas na Afirka ne kawai suka dakatar da azabtar da yara, inda Afirka ta Kudu ta kasance karshe ta baya-bayan nan da ta shiga sahu a watan Satumba. Sai dai Burundi da Burkina Faso suna ci gaba da ba da izinin hukunta yara a gida ta hanyar. Yayin da Togo ta kasance ta farko a Afirka a 2007 da ta hana dukan yara kwata-kwata a gida ko a makaranta.