1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF: Yara na fuskantar barazana

Abdul-raheem Hassan
November 18, 2019

Rahoton cika shekaru 30 da samar da 'yancin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana samun karuwar dadewar yara cikin koshin lafiya, amma har yanzu akwai wasu matsaloli da ke wa yaran barazana.

https://p.dw.com/p/3TCzZ
Angola Migration l Flüchtlinge aus dem Kongo in Cacanda bei Dundo
Hoto: picture alliance/Unicef/dpa/M. Gonzalez

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce baya ga matsalolin rashin ilimi da lafiya da abinci mai gina jiki da ke addabar yara, sauyin yanayi da cin zarafi ta yanar gizo na cikin manyan kalubale da ke shafar kananan yara a sassa daban-daban na duniya.

Cikin shekaru 30 an samu raguwar mace-macen kananan yara kasa da shekaru biyar da kusan kashi 60 cikin 100, yara da dama na zuwa akalla makarantar firamare kuma kasashe da dama sun amince da dokokin kare kananan yara.