1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cutar kanjamau a duniya

November 21, 2005
https://p.dw.com/p/BvKA

Wani sabon rahoto na majalisar dinkin duniyaya yayi nuni da cewa yaduwar kwayar cutar kanjamau na kara taázzara a tsakanin jamaá. Hukumar majalisar dinkin duniya akan yaki da cutar kanjamau ta yi kiyasin cewa a yanzu haka, mutane kimanin miliyan 40 ne dauke da kwayar cutar a duniya baki daya. Bugu da kari hukumar ta ce a wannan shekarar ta 2005 an sami karuwar mutane miliyan biyar wadanda suka kamu da cutar yayin da kuma wasu mutane miliyan uku ciki har da kananan yara dubu dari biyar suka rasu a sanadiyar cutar ta kanjamau, Hukumar ta majalisar dinkin duniya akan yaki da cutar kanjamau ta yi gargadi da yawan yaduwar cutar a gabashin turai da kuma kudancin Asia.

Rahoton ya kuma ce har yanzu nahiyar Afrika shi ne ya fi fuskantar annobar wannan ciwo inda aka kiyasta cewa kashi biyu bisa uku na alúmomin yankin suke dauke da kwayar cutar ta HIV / AIDS. Sai dai kumka a hannu guda rahoton ya baiyana cewa a yanzu mutane da dama a kasashe daban daban na duniya na iya samun maganin nan na Anti – Retroviral wanda ke rage radadin ciwon.