1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yajin aiki ya tilasta rufe filin jirgin saman Frankfurt

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 6, 2024

Gamayyar kungiyoyin kwadagon Jamus VERDI ta yi kira ga su ma'aikatan kamfanin sufurin jiragen Lufthansa da su ma su shiga yajin aikin a Larabar nan, domin neman karin albashi

https://p.dw.com/p/4dEKL
Hoto: Michael Probst/AP/picture alliance

Yajin aikin jami'an tsaron filin jirgin saman Frankfurt da ke nan Jamus ya tilasta rufe shi daga ranar Alhamis, kamar yadda mai magana da yawun hukumar kula da filin jirgin ya sanar a Larabar nan.

Karin bayani:An bude sabon filin jirgin sama a Berlin

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya rawaito filin jirgin na kira ga fasinjoji da su tuntubi kamfanonin jiragensu don jin karin bayanin inda za su sauka, domin babu damar sauka a Frankfurt.

Kuma tuni aka soke saukar jirage 650 a Larabar nan.

Karin bayani:'Yan sandan Jamus sun gano sakon kai hari a kasar

Gamayyar kungiyoyin kwadagon Jamus VERDI ta yi kira ga su ma'aikatan kamfanin sufurin jiragen Lufthansa da su ma su shiga yajin aikin a Larabar nan, domin neman karin albashi.