Birnin Frankfurt na nan a jihar Hesse da ke yamamcin tarayyar Jamus. Birnin na da yawan jama'a da suka kai dubu 700.
Frankfurt na daya daga cikin biranen Jamus da ke da girman gaske kana yana daya daga cikin birane da ke da muhimmanci ta fuskar tattalin arziki. Galibin cibiyoyi na kudi a Jamus na da hedikwatarsu ne a birnin sannan babban bankin Turai ma na da mazauninsa ne a birnin na Frankfurt.