Frankfurt: Ana duba lafiyar pasinjoji daga Wuhan | Labarai | DW | 01.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Frankfurt: Ana duba lafiyar pasinjoji daga Wuhan

Wani jirgin sama daga birnin Wuhan dauke da pasinjoji Jamusawa da 'yan wasu kasashe sama da 100, ya sauka a birnin Frankfurt cibiyar kasuwancin Tarayyar Jamus.

An samu jinkirin isowar jirgin da ke dauke da Jamusawa 102 da 'yan wasu kasashe 26 ne, biyo bayan kin amince wa jirgin sauka don kara mai da Rasha ta yi.

Mahukuntan Rashan dai sun nunar da cewar, filin jiragen saman Moscow bashi da sukunin karbar jirgin na Jamus, hakan ya tilasta jirgin sauka a birnin Helsinki na kasar Finland.

Za'a binciki lafiyar dukkan pasinjojin domin tabbatar da cewar basu da kwayar cutar Corona da ta kashe mutane 259 kawo yanzu a kasar China, a wata cibiya ta musamman da aka kebe a filin jirgin saman na birnin Farankfurt.