1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara sabuwar kakar lig-lig a Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
September 21, 2020

Kungiyoyin Bayern da Dortmund da Herther da Ausburg da Hoffenheim da Leipzig, sun fara kakar lig-lig na Jamus wato Bundesliga da kafar dama.

https://p.dw.com/p/3iniO
Fußball Bundesliga VfL Wolfsburg - Bayer 04 Leverkusen
Hoto: Peter Niedung/NurPhoto/picture alliance

Za mu fara da batun gasar tseren keke ta duniya da ake wa lakabi da Tour de France, inda 'yan kasar Sulobeniya biyu suka zama zakaran gwajin dafi a gasar ta bana. Mintoci kalilan bayan da Tadej Pogacar da Primoz Roglic suka kare gasar a matsayin na daya da na biyu, shugaban kasar Sulobeniyan Borut Pahor ya bayyana nasarar a matsayin abin da tarihin kasar ba zai taba mantawa da shi ba. Tadej Pogacar ya kasance wanda ya lashe gasar yana da mafi karancin shekaru, tun bayan dan kasar Ireland  Sam Bennett da shi ma ya lashe gasar da karancin shekaru a shekarar 1904.

Mai shekaru 21 a duniya dai, Pogacar ya bayyana cewa babu abin da zai cewa magoya bayansa bayan dimbin godiya, domin kuwa sun nuna masa kauna cikin makonnin da aka kwashe ana gudanar da gasar. Primoz Roglic dan kasar ta Sulobeniya da ya kasance gwarzon gasar tseren kekunan na tsawon lokaci, ya zo na biyu yayin da Richie Porte dan kasar Ostreliya ya zo matsayi na uku.

Tadej Pogacar (tsakiya) da ya lashe gasar tseren keken Tour de France a shekarar 2020
Tadej Pogacar (tsakiya) da ya lashe gasar tseren keken Tour de France a shekarar 2020Hoto: Stephane Mahe/Reuters

Tuni dai Pogacar ya samu kyautar taya murna ta zunzurutun kudi Euro 623,930 a matsayin godiya daga 'yan kungiyarsa ta Hadaddiyar Daular Larabawa. A wannan Litinin din ne dai Pogacara ke cika shekaru 22 a duniya.

Kakar wasannin lig-lig na Bundesliga a shekarar 2020/2021

A karshen makon da ya gabata ne aka dawo kakar wasannin Bundesligar Jamus, inda a ranar Jumma'a kungiyar kwallon kafa ta Bayern da ke rike da kambun na Bundesliga, da kuma ta lashe kofin sau bakwai a jere, ta yi wa kungiyar kwallon kafa ta Schalke dakan gumba da ci takwas da nema. A ranar Asabar kuwa, kusan kafatanin kungiyoyin da suka karbi bakunci, kwallon ba ta yi musu rana ba, domin kuwa in ban da kungiyar Borussia Dormund da ta lallasa Borussia Mönschengladbach da ci uku da nema da kuma Frankfurt da ta sha da kyar da kunnen doki daya da daya da kungiyar da ta hauro kakar Bundesligar matakin farko a bana, wato Arminia Bielefeld, sauran kungiyon dai an je garinsu ne an kuma fi su iya taka rawa. Ga misali Freiburg ta bi Stuttgart har gida ta lallasa ta da ci uku da biyu yayin da Hoffenheim ta bi FC Kolon gida ta kuma samu nasara da ci uku da biyu.

Dan wasan Bayern Leroy Sane (hagu) yana murnar zura kwallo ta hudu da kungiyarsa ta yi a ragar Schalke
Dan wasan Bayern Leroy Sane (hagu) yana murnar zura kwallo ta hudu da kungiyarsa ta yi a ragar SchalkeHoto: Matthias Schrader/P Photo/picture alliance

Haka abin ya kasance a birnin Berlin, inda Ausburg ta bi Union Berlin gida ta yi mata dukan kawo wuka da ci uku da daya. Wasan da ya fi daukar hankali kuma ya bayar da mamaki shi ne wanda aka fafata tsakanin Werder Bremen da Hertha Berlin, domin kuwa Berlin din ta kafa tarihi, ko kuma in ce ta rushe tarihin yadda Bremen ke samun galaba a kanta duk lokacin da ta kai ziyara birnin. A wannan karon dai Hertha ta yi wa Bremen din lilis da ci hudu da daya, kuma wannan wasan ne ma muka kawo muku kai tsaye daga nan sashen Hausa na DW a ranar ta Asabar. A ranar Lahadi kuwa, kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig ta karbi bakuncin Mainz, inda kuma ta samu nasara a kanta da ci uku da daya, yayin da aka tashi babu ci a filin wasa na Wolfsburg, a karawarta tsakaninta da Leverkussen.

Najeriya ta haura matsayi na 29 a jadawalin FIFA

Najeriya ta samu ci gaba a jadawalin kasashen da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA take fitarwa duk bayan watanni shida inda ta haura zuwa ta ishirin da tara daga matsayi na talatin da daya a duniya yayinda a nahiyar Afirka kuwa ba ta sauya zani ba inda ta ke nan a matsayin ta na uku a bayan Senegal da Tunisia.

Shugaban hukumar kula da kwallon zari ruga na kasar Faransa, Bernard Laporte zai gurfana gaban hukumar yaki da almundahana domin amsa tambayoyi. Bayanai sun nunar da cewa ana zargin Laporte da kulla alaka da mai kungiyar kwallon zari ruga ta Montpellier Mohed Altrad. Laporte zai amsa tambayoyin ne karkashin binciken da ofishin mai shigar da kara kan abin da ya danganci kudi ya fara a shekara ta 2017, biyo bayan wani rahoto da masu bincike na ma'aikatar wasannin kasar Faransan suka kai. Laporte dai shi ne mataimakin shugaban Hukumar Kula da Kwallon Zari Ruga na Duniya, ana zarginsa da nuna son kai, bayan da wani kamfanin mallakarsa ya sanya hannu kan wata kwantiragi da rukunin kamfanonin Altrad a farkon shekara ta 2017.