Warware rikicin cikin gida a jam′iyyun siyasar Najeriya | Siyasa | DW | 26.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Warware rikicin cikin gida a jam'iyyun siyasar Najeriya

Yayin da jam'iyyun siyasa a Najeriya suka kammala fid da 'yan takara a matakai daban-daban na zaben 2015, hakan ya haifar da gunaguni tsakanin 'ya'yan wasu jam'iyyun.

Wannan matsalar dai ta fi yawa a tsakanin manyan jam'iyyun kasar wato PDP da APC. Tun farko dai an samu wasu da suka canja sheka daga wata jam'iyya zuwa wata. Bisa wannan dalili ne kuwa shugabanni da 'yan siyasa ke ci gaba da kokarin shawo kan wadanda ake gani an yi wa laifi don kada su fice daga jam'iyyarsu ta asali.

Hakan dai na zuwa ne yayin da ya rage kasa da watanni biyu a gudanar da zabuka a tarayyar ta Najeriya. Wanda kuma ke zama wani nakasu ga masu rike da madafun iko kuma suke neman yin tazarce. Baya da a yanzu 'yan siyasa ke ci gaba da fadi tashi don samun magoya baya na kaiwa gaci, wasu kuwa na ci gaba da shailar cewa lalle sai an yi zubar gade kowa ya rasa.

Kokarin shawo kan magoya baya

Yanzu haka dai jam'iyyar PDP da ke mulki a Najeriya da kuma babbar jam'iyyar adawa ta APC sun daura damarar sulhunta magoya baya. Jihar Legas ga misali wadda ta kasance hannun 'yan adawa tun bayan da Najeriya ta koma tafarkin demokradiyya a shekarar 1999, bisa ga dukkan alamu a zaben 2015 za a yi kare jini biri jini ne tsakanain APC da PDP.

Nigeria Vizepräsident Namadi Sambo

Namadi Sambo, mataimakin shugaban Najeriya

A cikin wannan makon ne ma mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Namadi Sambo ya yi tattaki zuwa birnin na Legas, domin warware irin wannan dambarwar siyasa ta cikin gida. A cewarsa dai yanzu wannan rikici na cikin gida ya zama tarihi, domin "an hadu an tattauna, an kuma dinke barakar da ke akwai, kowa ya yi alkawari zai yi aiki da jam'iyya."

Abin jira a gani na zama irin tasirin da irin wannan sasantawa ta cikin gida za ta yi gabanin zaben na farkon shekarar 2015 a tarayyar ta Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin