1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu jam'iyyun Nijar sun goyi bayan Bazoum

Gazali Abdou Tasawa MNA
January 4, 2021

Jam’iyyun siyasa da suka kama wa Bazoum Mohamed dan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya a zagayen farko na zaben shugaban kasa sun jaddada goyon bayansu gare shi.

https://p.dw.com/p/3nVJP
Wahlen Niger Niamey | Präsidentschaftskandidat  Mohamed Bazoum
Hoto: Issouf SANOGO/AFP

A sanarwar da ya fitar a wannan rana a lokacin wani kasaitaccen biki da ya shirya a babbar cibiyar jam'iyyar PNDS Tarayya ta kasa da ke a birnin Yamai, kawancen jam'iyyun siyasa kimanin 50 na Coalition Bazoum 2021, wanda ya kama wa dan takara Bazoum Mohamed a zagayen farko na zaben shugaban kasa, ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da kawo masa goyon baya, tare kuma da yin kira ga sauran jam'iyyu mambobin kawancen MRN irin su Jamhuriyar ta Albade Abouba da ma na APR irin su MNSD Nasara, wadanda ba sa tare da su a zagayen farko kasancewa suna da nasu dan takara, da su zo a yanzu su shiga wannan kawance don ganin dan takarar nasu ya lashe zaben a zagaye na biyu, kamar yadda Alhaji Yahouza Sadissou na Madobi shi ne shugaban jam'iyyar Bazara mamba a kawancen na Coalition Bazoum 2021 ya bayyana.

Karin bayani: Zaben Nijar zakaran gwajin dafi

Da yake tsokaci a gaban manema labarai a karshen wannan sanarwa, dan takarar jam'iyyar ta PNDS Tarayya Malam Bazoum Mohamed, bayan nuna gamsuwarsa da goyon bayan da ya samu, ya bayyana fa'idar da ke tattare da kiran da jam'iyyun kawancen suka yi wa sauran jam'iyyu abokan tafiyarsu a cikin gwamnatin Alhaji Mahamadou issoufou.

Yahouza Sadissou Madobi shugaban jam'iyyar Bazara kuma mamba a kawancen Coalition Bazoum 2021
Yahouza Sadissou Madobi shugaban jam'iyyar Bazara kuma mamba a kawancen Coalition Bazoum 2021Hoto: DW/A. Mamane

Jam'iyyar MNSD Nasara wacce ke a jerin jam'iyyun da a baya-bayan nan suka kalubalanci sahihancin takardar dan kasa ta Bazoum Mohamed kafin tafiya zagayen farko, na daga cikin jerin jam'iyyun da kawancen na Coalition Bazoum 2021 ke yi wa kyarkyara. Sai dai wasu labarai da ke yawo a shafukan sada zumunta na cewa jam'iyyar ta MNSD Nasara ta kulla wani sabon kawance da MPR Jamhuriya da kuma PJP Dubara ta Janar Salou Djibo, kana sun yanke kauna a game da yiwuwar yin duk wani kawance da Tarayya. Sai dai Rabiou Hassan Yari mataimakin shugaban yakin neman zaben jam'iyyar ta MNSD Nasara ya ce jita-jitar da ake yadawa ba gaskiya ba ce kuma ba su yanke kauna ba da wata jam'iyya.

Karin bayani: Za a je zagaye na biyu a zaɓen ƙasa na Nijar

Yanzu dai kowane daga cikin 'yan takarar biyu ya dukufa ta bayan fage wajen zawarcin jam'iyyun da za su kama masa a kokowar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa. A yayin da 'yan kasa suka zura ido su ga irin tumka da warwarewar da zai wakana a tsakanin jam'iyyun wajen kafa kawancen goyon bayan 'yan takarar biyu, kamar yadda aka saba gani a duk lokacin da za a tafi zagaye na biyu a zaben shugaban kasa a tarihin siyasar kasar ta Nijar.