1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Shugaba Zelenskyy na daf da jingine batun shiga NATO

Abdoulaye Mamane Amadou
December 14, 2025

A kokarin sulhunta yakin Ukraine da Rasha, shugaba Volodymyr Zelenskyy ya nuna alamar bayar da kai game da yunkurin shiga NATO idan ya samu tabbacin tsaro daga yammacin Turai.

https://p.dw.com/p/55Kt9
Berlin na kasar Jamus Shugaba Selenskyj da Friedrich Merz da manzon Amurka Witkoff
Berlin na kasar Jamus Shugaba Selenskyj da Friedrich Merz da manzon Amurka WitkoffHoto: Guido Bergmann/Bundesregierung/dpa/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bayyana cewa a shirye yake ya yi watsi da yunkurin shiga kungiyar tsaro ta NATO a wani mataki na samun tabbacin tsaro daga yammacin Turai.

Rasha ta kai munanan hare-hare a kudancin Ukraine

Sai dai da yake tattaunawa da wakilan Amurka da wasu shugabannin Turai a birnin Berlin fadar gwamnatin Jmaus kan kawo karshen yakin Ukraine da Rasha, Zelenskyy ya ki mika wuya kan yunkurin Amurka na mallaka wa Moscow wasu yankunan Ukraine kamar yadda Trump ya bukata cikin daftarin sharwarin kawo karshen yakin.

Zelensky zai gana da shugabannin EU kan yakin Rasha

Shugaban Ukraine ya zargi Rasha da kai hare-hare da jiragen sama marasa matuki sama da 1,500 da bama-bamai da makamai masu linzami ciki har da na daren ranar Asabar, wanda ya shafi tashar jiragen ruwa na Odesa, sama da mutane miliyan daya ba su wutar lantarki.