Turkiya na janye sojoji daga Iraki
December 14, 2015Talla
A yayin mayar da martani kan matakin da Turkiyan ta dauka Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier yayi nuni da cewar:
Yau mun ga alamun farko a inda Turkiya ta bayyana janye sojoji daga Iraki, Ina fata hakan zai kawo karshen zaman yanayin dardar a daukacin yankin, ba za kuma mu amince da wani rikici a yankin ba.
A wannan watan ne dai Iraki ta nuna rashin jin dadi bayan da Turkiyan ta jibge sojoji 150 gami da wasu tankokin yaki 25 a kusa da Mosul wanda ya sanya kasashen Amirka da Jamus daukar wani matakin sasanta takaddamar domin hada hannu wuri guda domin yakar kungiyar IS.